Babban bankin Najeriya, CBN, ya mayar da martani ga labarin da aka samu kan tashar yanar gizon daukar ma’aikata,Daily Post ta rawaito.
Isa Abdulmumin, Mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN a cikin wata sanarwa da ya fitar ya karyata labarin a ranar Alhamis, yana mai bayyana tashar daukar ma’aikata ta yanar gizo a matsayin ta bogi kuma marar tushe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kashi 30% Na Mambobin NASS Suka Dawo; Mun Rasa Iya Aiki, Lawan Ya Koka
Babban bankin ya fayyace cewa ba ya gudanar da wani aiki na daukar ma’aikata gaba daya kuma ba zai taba neman BVN na masu bukata ba ko kuma nuna wariya ga masu nakasa.
Kazalika ya shawarci ‘yan Najeriya da su lura da ayyukan ‘yan damfara.
“Don kaucewa shakku, a halin yanzu CBN ba ya gudanar da wani aikin daukar ma’aikata gaba daya,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Fara Gudanar Da Aikin Umara A Garin Makka Na Saudiyya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar gudanar da aikin Umrah, cikin tsauraran matakan tsaro, bayan isowarsa babban masallacin Juma’a na Makkah.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa shugaban kasar tare da tawagarsa sun samu jagorancin tawagar fadar Sarkin Saudiyya mai kula da harkokin babban masallacin da kuma ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na Najeriya Farfesa Isa Pantami a wajen yin ibadar.
A baya dai shugaban na Najeriya ya ziyarci wasu wuraren ibada na tarihi a Madina a ranakun Talata da Laraba kafin ya wuce Makkah domin yin aikin Umrah.
Haka kuma shugaba Buhari ya ziyarci masallacin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam.