Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, ya taya abokin hamayyar sa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) murnar lashe zabe, Abba Kabir Yusuf, (wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida).kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Idan ba a manta ba, Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Yusuf a matsayin zababben gwamna, sanarwar da Gawuna da jam’iyyar sa suka kalubalanta.
KARANTA WANNAN LABARIN: May 29: Buhari ba zai kara ko kwana daya a Ofishinsa ba — Boss Mustapha
Amma ‘yan sa’o’i kadan da zababben gwamnan ya karbi takardar shaidar cin zabe, Gawuna’ ya taya shi murnar nasarar da ya samu.
A jawabinsa na karbar takardar shaidar cin zabe, Yusuf ya yi kira ga Gawuna da ya tabbatar da furucin da ya yi a baya cewa zai amince da sakamakon zaben a matsayin ikon Allah.
Da yake amsa wannan kiran, Gawuna a cikin wani sakon murya da babban sakataren yada labaransa ya rabawa manema labarai, ya ce yayin da yake tabbatar da furucin da ya yi tun farko kan ikon Allah, yana addu’ar Allah ya taimaki Yusuf ya zama shugaba na gaskiya ga kowa da kowa, wanda zai yi zama mai adalci ga kowa.
“Ina so in tunatar da al’ummar jihar Kano cewa, tun da farko a lokacin yakin neman zabe, mun yi addu’a cewa idan muka ci zabe shi ne mafi alheri a gare mu, Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu, idan kuma ba haka ba, Allah Ya ba mu abin da ya dace da mu.
“Don haka ina kira ga mabiyana da magoya bayana da su amince da kaddarar da ta zo mana. Ga wanda ya ci zabe, ina yi masa addu’a ya zama shugaba nagari wanda zai yi adalci ga kowa. Mu, Allah Ta’ala Ya yi mana jagora don mu zama masu bin shugabanninmu nagari,” in ji Gawuna.
A wani labarin kuma, DSS Ta Bankado Wani Mummunan Makircin Da Ake Shiryawa Kasar nan
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Laraba ta ce ta gano wasu manyan mutane dake shirin shirin kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ma’aikatar tsaron sirrin ta bayyana hakan ne a jerin sakonnin da ta wallafa a shafinta na twitter ranar Laraba.