Shugabannin kungiyoyin al’adu na jihar Benuwe da shugabannin kabilu sun sha alwashin yin tir da duk wani shiri da gwamnatin tarayya za ta yi na ginawa Fulani makiyaya gidaje da matsugunnai a kowane yanki na jihar ta ko wane bangare.
Shugabannin sun yi nuni da cewa sanarwar cikin gaggawa da gwamnatin tarayya ta yi na aniyar ta na gina gidaje 1,000 a jihohi bakwai da suka hada da Binuwai ta afkawa barna kuma ba za a yi maraba da ita a jihar ba.
Karanta nanTinubu Na Son Karkatar Da Hankalin Yan Najeriya Su Manta Matsin Rayuwar Da Suke Ciki-Atiku
A cikin wata sanarwa da suka fitar a karshen mako mai dauke da sa hannun shugaban na Mzough U Tiv, MUT, (Woridwide) Iorbee Ihagh da shugaban Ochetoha k’Idoma, OKI, AVM Toni Adokwu (mai ritaya).
Shugabannin sun tabbatar da cewa babu wani bangare na kungiyar. Za a bai wa jihar domin gina gidaje da matsugunan da za su zaunar da Fulani makiyaya yayin da sama da ‘yan asalin jihar Benue miliyan biyu ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke warwatse a fadin jihar.
Shugabannin sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aikin wanda ta ce wani shiri ne na yaki da tashe-tashen hankula a yankin Arewacin kasar nan, kuma za a samar da kayayyakin aiki kamar makarantu, dakunan shan magani, likitocin dabbobi da wuraren kiwo na al’ummar Fulani.
Amma, ko da a ce za a yi, dole ace Gwamnatin Tarayya ta zaunar da yan gudun hijira a Jihar, kafin ta yi tunanin kawo bare ta kuma samar musu da mafaka a cikin Jihar.
Don kaucewa shakku, jihar Binuwai na da ‘yan gudun hijira sama da miliyan biyu da gwamnati ta yi watsi da su da su halaka a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar.
A wani labarin kumaShugaba Tinubu Ya Nada Jamila Bio Ibrahim A Matsayin Ministar Matasa
Shugabannin sun ja hankalin shugaba Tinubu kan halin da ake ciki a gundumar Moon Council na karamar hukumar Kwande, inda aka kori mutanen yankin tare da mamaye gidajensu da wasu makiyaya dauke da makamai.
Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga lamarin tare da rungumar dokar kiwo ta jihar Binuwai domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a jihar.