Gidauniyar Uba Sani ta dauki nauyin biyan kudin tiyatar da ake yi wa wasu tagwaye yara mata da aka Haifa a hade a babban asibitin kasa dake Abuja.
Shugaban kungiyar amintattu kuma wanda ya kafa gidauniyar Sanata Uba Sani ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci asibitin domin gane wa idonsa halin da tagwayen da mahaifiyarsu ke ciki.
Ya kuma tabbatar wa da mahukuntan asibitin cewa gidauniyar sa za ta biya dukkan kudaden da ake kashewa wajen yi wa tagwayen aikin fi’da da kula da tagwayen da mahaifiyarsu a lokacin zamansu a asibitin.
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, inda mahaifan tagwayen suka fito, ya kuma bukaci likitocin asibitin da su fada masa kudin tiyatar kala uku da za a yi wa tagwayen domin raba su.
Mahaifin tagwayen Malam Umar Rayyanu ya mika godiya ga gidauniyar da shugabanta Sanata Uba sani bisa daukar nauyin gudanar da ayyukan da za su ceto rayuwar tagwayen da aka haifa masa, ya kara da cewa “wannan karamcin dole ya Sanya farin ciki da murmushi a fuskarsa, da mahaifiyar su da sauran ‘yan uwa da abokan arziki inji Mahaifin tagwayen
“Muna matukar godiya ga Sanata Uba Sani bisa wannan karamcin da ya nuna mana, kuma mun jin dadin ziyarar da ya kawo mana, Allah Ya saka masa da alheri,” in ji mahaifin tagwayen.
An haifi tagwayen ne ta hanyar tiyata a makon da ya gabata a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna wanda daga bisani Kuma likitoci sun mika iyayensu zuwa asibitin kasa da ke Abuja domin ci gaba da kula da lafiyarsu.
Gidauniyar Uba Sani, da ta samu labarin lamarin shine ta garzaya domin bayar da tallafin jinya wanda ta saba yi wa marasa lafiya da ke fama da barazanar rayuwa musamman wadanda ba su da hanyar samun isasshen magani.
Sanata Uba Sani ya samu rakiyar Babban Daraktan Gidauniyar Uba Sani, Malam Ibrahim Dan Halilu.
A halin yanzu, aikin farko da aka yi a an bayyana shi amatsayin ayyukan nasara.
Comments 1