Wata tartsatsin igiyar wutar lantarki sakamakon hadewar wayoyin wutar Lantarki, wanda ya haddasa gobara da ta kone wani bene mai hawa 12 a garin Ilorin na jihar Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar da ta tashi a ranar Juma’a, a wani gini mai daki 12 da ke kan titin Afon 17 a unguwar Sabo Oke na garin Ilorin, ta yi sanadin asarar dukiya mai tarin yawa, yayin da mazauna garin suka yunkuro domin dakile ta, tare da jikkata wasu.
Da take tofa albarkacin bakinta, mai gidan, Misis A. Ibitoye, ta nemi goyon bayan gwamnatin jihar da hukumomin da abin ya shafa domin talfawa wadanda abin ya shafa duba da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
A nasa martanin, Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya ce, “Ko da yake gobarar ta yi yawa, amma mutanena sun yi kokari, wajen kashe ta.