Wani ginin makaranta mai hawa daya da ke Agbado a karamar hukumar Ifo a jihar Ogun ya ruguje a ranar Asabar da yamma biyo bayan shafe wani lokaci ana shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya, Punch ta rawaito.
Wakilinmu ya tattaro cewa ginin da abin ya shafa ya kunshi ajujuwa goma na makarantar sakandaren gundumar Agbado da ke yankin Ifo a jihar.
KARANTA WANNAN: Zulum Ya Kai Wata Ziyarar Ba Zata Asibiti Tsakar Dare
Ginin ya ruguje ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da akayi a ranar Asabar wanda kuma ya lalata wasu hanyoyi a yankin.
An kuma tattaro cewa tsohon Sanata Iyabo Obasanjo-Bello ne ya bayar da gudummawar ginin a matsayin daya daga cikin ayyukan mazabarsa a lokacin da yake wakiltar mazabar Ogun ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2007 zuwa 2011.
Wata majiya a yankin ta ce ginin ya sha fama da rashin kulawa na tsawon shekaru bayan an yi watsi da shi.
Majiyar ta kara da cewa gwamnatin jihar ba ta taba amfani da ginin ba.
Wani mazaunin unguwar, Kolawole Adelani, wanda ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi, ya ce ginin kafin ya ruguje ya zama babbar barazana ga rayuwar daliban da ma’aikatan makarantar.
Adelani ya ce wasu mazauna makarantar sun ja hankalin gwamnatin jihar kan tabarbarewar ababen more rayuwa na makarantar.
Adelani ya bayyana lamarin a matsayin ” bala’in da aka dade ana jira ya faru.”
Ya ce, “Gini ya kwashe sama da shekaru 15 yana nan yana fama da matsalolin.
“Kowa ya ji tsoron cewa irin wannan bala’i na nan afkuwa kusa ba da nisa ba. Alhamdu lillahi, ba a rasa rayuka ba.”
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban gundumar Agbado, Ganiyu Olowu a nasa martanin ya koka da cewa an yi hasashen rushewar ginin tun kafin faruwar lamarin.
Olowu ya ce, “Yau (Asabar) biyo bayan saukar ruwan sama da rana, wani dogon zango na ajujuwa da yawa ya ruguje a makarantar mu mai hawa daya ta Alma Mater Comprehensive High School dake Oke Aro.”
Ya ce kungiyar tsofaffin daliban ta sha sanar da ma’aikatar ilimi ta jihar game da tabarbarewar ginin da kuma hadarin da ke tattare da shi ga dalibai.
“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki da ke aiki tare da gwamnatin jihar don tabbatar da ingantaccen ilimi a fadin jihar, mun jawo hankalin tsohon kwamishinan don ya zo yaga yanayin ginin,” in ji shi.
A wani labarin kuma, NDLEA Ta Kama Wata Lauya, Da Wasu Dauke Da Tarin Miyagun Kwayoyi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wata lauya mai suna Ebikpolade Helen, wacce ta kware wajen hadawa da rarraba skuchies, da cakuda wiwi, da wasu miyagun kwayoyi.
Wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadin nan a Abuja, ta ce matar tana zaune ne a unguwar Lekki da ke jihar Legas.