- Girgizar kasa mai karfin awo 5.0 ta afku a birni mafi girma a Afirka ta Kudu.
- Girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 00:38 na dare agogon GMT mai zurfin kilomita 10.
- Girgizar kasar ta akfu da sanyin safiyar ranara Lahadi
Girgizar kasa mai karfin awo 5.0 ta afku a birnin Johannesburg mafi girma a Afirka ta Kudu da sanyin safiyar Lahadi, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka (USGS) ta ce girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 00:38 na dare agogon GMT mai zurfin kilomita 10 (mil 6).
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Benue Ta Kafa Wani Kwamiti Domin Kwato Kadarorin Gwamnati Da Aka Wawure
Rahoton ya ce wasu mazauna birnin Johannesburg sun bayar da rahoton jin karar girgizar kasar.
Daya daga cikin mazauna garin ya rubuta a shafin Twitter, cewa “Girgizar kasa a Johannesburg. Mafi zurfi da ƙarfi na ji! Ta kasance kusan sakanni 30. ”
Sai dai kuma, kungiyar tuntuba da kasadar tsaro da magance rikice-rikice Crisis24 ta ce babu wani bayanan barna ko asarar rayuka sakamakon girgizar kasar.
A wani labarin kuma, FG Ta Kashe Sama Da Biliyan 400 Don Biyan Bashi A Watan Fabrairu
Gwamnatin tarayya ta kashe kashi 85.37 na kudaden shigar da ta samu, wajen biyan basussukan da ake bin ta a watan Fabrairu, kamar yadda PUNCH ta gano.
Babban bankin Najeriya, a rahotonsa na wata-wata na tattalin arziki na watan Fabrairun 2023, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga na N478.57bn a watan Fabrairu.