An samu tashin gobara a hedikwatar hukumar yi wa kasa hidima dake birnin tarayya Abuja ranar Juma’a.
Hukumar ta ce ba a samu asarar rai ba sakamakon barkewar gobarar kwatsam domin ta takaita ne a hawa na uku na ginin bene mai hawa shida.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Dauke Da Sassan Jikin Dan Adam
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai, Eddy Megwa, ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce nan take ofishin babban birnin tarayya da na hukumar kashe gobara ta tarayya suka kashe gobarar a lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe 07:30 na safe.
Megwa ya kuma ce benen da abin ya shafa na cikin tsare-tsare, bincike da kididdiga da kuma babban ma’aikata inda gobarar ta shafi wani daki ne kawai da na’urorin lantarki.
Ya ce, “An yi sa’a, ba a yi asarar rai ba kuma an kwashe dukkan muhimman takardu da gaggawa kuma an kiyaye su.
“Masu gudanar da shirin suna godiya sosai ga Ma’aikatar kashe gobara ta Tarayya da FCT saboda yadda suka mayar da martani cikin gaggawa wanda ya rage tasirin lamarin.
“Hukumar ta kuma yaba wa dukkan hukumomin tsaro bisa gagarimar rawar da suka taka a lokacin da lamarin ya faru.” NAN
A wani labarin kuma, Daliban Da Suka Dawo Daga Ukraine: Iyaye Sun Yi Zargin Biyan Kuɗin Karatu Sau Biyu Ga Jami’o’i
Iyayen daliban Najeriya da aka kwaso daga kasar Ukraine sakamakon yakin da ake yi da kasar Rasha sun koka da yadda aka rubanya kudin makaranta da ake zargin an biya domin ‘ya’yansu su ci gaba da karatunsu a Najeriya.
Wani mahaifi, Taofik Amade, wanda ya zanta da manema labarai a Abuja ranar Alhamis kan ci gaban, ya yi zargin cewa jami’o’in kasar Ukraine sun hana ‘ya’yansu zabin shiga jami’o’in da suke so ta hanyar kin sakin takardun karatunsu.
Maimakon haka, ya ce, sun shiga tsarin motsi da wasu jami’o’in Najeriya ta hanyar Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa inda daliban za su gudanar da laccoci a wani bangare ta yanar gizo tare da Ukraine da kuma tare da zababbun jami’o’in Najeriya.