An samu barkewar gobara a hedikwatar ma’aikatar kudi da ke Abuja da safiyar Laraba.
Babu labarin Cikakkun abubuwan da suka faru a yayin gobarar har lokacin hada wannan rahoton, amma shafukan sada zumunta sun nuna hayaki na ta turnuke ginin da ke tsakiyar cibiyar kasuwanci ta babban birnin Tarayya Abuja.
Jami’an kashe gobara na kokarin kashe wutan domin shawo kan gobarar da ta haifar da firgici a tsakanin ma’aikatan ma’aikatar.
Cikakkun bayanai na wannan rahoto na nan tafe.
A wani labarin Kuma na daban.
Har yanzu dai ba a san inda wasu yara biyar da wata mata ta sace ba wanda ta yi kama da malamar koyar da darasin gida a unguwar Rukpakulusi da ke garin Eliozu a jihar Ribas kwanaki 11 da faruwar lamarin.
Yaran biyar masu shekaru tsakanin watanni 18 zuwa hudu, wadanda ake zargin ta sace su ne bayan da ta bukaci su biyo ta inda za ta saya musu kayan rubutu.
Mahaifin yaran biyu, Mista Emmanuel Benjamin, ya shaida wa jaridar PUNCH a ranar Talata cewa, ‘yan sanda a ofishin Okporo sun bukaci ya biya su kudi naira 200,000 domin a gaggauta yin bincike tare da gano wandanda ake zargin.
Emmanuel ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, inda ya ce bai san halin da yaran na sa da aka bayyana sunayensu da Idara da Emem ke ciki ba.
“Tun ranar ban ga ‘ya’yana ba. Ban ji dadi ba. Babu wanda bazai yi baƙin ciki ba idan irin haka ta same shi. Ba zan iya ko barci ba kuma ba na jin dadi ko kadan,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa ‘yan sanda sun bukaci iyalan dasu bada kudi domin a gaggauta yin bincike kan lamarin.
“Basa aiki akan wannan lamarin, Idan muka je sai suka ce mu kawo kudi.
“Na je ofishin ‘yan sanda na Okporo. Sai suka ce mu kawo kudi da lambar wayar da za su bibiyesu. Sai suka ce mu kawo Naira 200,000 don su nemo inda matar take zaune. Amma ba ni da irin wannan kuɗin. Ni ba babban mutum ba ne,” in ji Emmanuel.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, an kasa samun jin ta bakin kan lamarin.