Gwamantin Tarayya ta sha alwashin Tallafawa Manoman Citta da cutar Fungal ta illata Gonakinsu
Ministan ya tabbatar wa manoman Citta a Jihar Kaduna cewa Gwamnatin Tarayya zata tallafa masu don magance Cutar Fungal.
Ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ya tabbatar wa manoman Citta tallafin Gwamnati da cutar kwalara (Fungal) ta shafi amfanin gonakinsu a Jihar Kaduna kwanan nan.
Tabbacin Gwamnati na bayar da tallafin ya zo ne makonni kaɗan bayan Cutar Fungal ta lalata gonakin Citta sama da dari biyu da dukiyar ta kai kimanin naira Biliyan Goma a Kudancin Kaduna.
Ministan wanda ya samu wakilcin Mataimakin babban Jami’in noma na
Ma’aikatar noma da samar da abinci ta Tarayya, Mrs. Rita Agbogo, ta bayar da tabbacin Ministan na ɗaukar matakin gaggawar a lokacin da ta ziyarci gonakin da abin ya shafa a Kudancin Kaduna a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:An Fara Yunƙurin Hana Sana’ar Karuwanci Da Sayar da Muggan Ƙwayoyi A Wata Jihar Kudu
Wakilin Ministan wadda ita ce Shugabar tawagar Mutane biyar da Ministan ya aike zuwa Kudancin Kaduna ta jaddada kudirin Ma’aikatar na ganin an samar da dawwamammiyar mafita don hana sake afkuwar iftila’in da kuma tabbatar da ganin an baiwa manoman da abin ya shafa tallafin da ya dace.
Ta bayyana cewa, “Mun rigaya muna jin raɗaɗin da manoman Citta suka ji, kuma shi ya sa muke nan kan aikin tantance ɓarnar da cutar yi.
Da ziyarar da muka kai wasu filayen noma mun ga irin ɓarnar da aka yi, kuma za mu ba wa ma’aikatar shawara kan wace hanya ce mafi dacewa da za a taimaka wa manoman da abin ya shafa daga halin da ake ciki yanzu”.
Da aka tambaye ta ko me ka iya zama sanadin cutar fungal ɗin, sai ta ce, “kamar yadda muke magana a yanzu ba mu san musabbabin ɓarnar ba, kuma shi ya sa muke tare da sauran ƙungiyoyin da abin ya shafa.
Za mu yi bincike kuma mu ci gaba da cuɗanya da waɗannan kungiyoyi domin sanin musabbabin da kuma hana faruwar hakan nan gaba”.