By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jajantawa mabiya addinin kirista bisa rasuwar shugaban kungiyar kiristoci ta jihar, Reverend Paul Olawoore.
Olawoore, wanda shi ne Bishop na Diocese na Ilorin na cocin Katolika kuma shugaban kungiyar CAN na jihar, ya rasu ne a safiyar ranar Asabar yana da shekaru 60 a duniya.
Wata sanarwa da kungiyar yada labaran Katolika ta Najeriya ta fitar mai dauke da sa hannun hadin gwiwar shugabanta na kasa, Patrick Obu; da Babban Sakatare, Peter Dada, ya ce mutuwar Olawoore ta faru ne kwatsam.
Sanarwar ta’aziyyar ta ce, “Shugaban kungiyar na kasa, majalisar zartarwa ta kasa da kuma mambobin kungiyar yada labaran Katolika ta Najeriya sun mika ta’aziyyarsu ga cocin Katolika na Ilorin, bisa rasuwar Bishop Paul Olawoore.”