Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da makamai domin yakar ‘yan bindigar da ke addabarsu.
A cewar gwamnan, jami’an tsaro kadai ba za su iya magance matsalar jihar ba.
Masari ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai a Katsina cewa jami’an tsaron jihar ba su isa su shawo kan lamarin ba.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa wadanda suke da niyyar mallakar bindigogi domin su taimaka wajen dakile matsalar ‘yan fashin daji da ta addabi jihar.
“Za mu goyi bayan wadanda suka zo da shirin sayo makamai saboda mazauna yankin na bukatar su kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro. Wadannan mutane (jami’an tsaro) ba su da adadin da za su kare jama’a”.
Gwamnan ya ce ‘yan sanda za su yi rajistar duk bindigogin da mazauna garin suka saya domin tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata.
Ana ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a Katsina, da kuma wasu jihohin Arewa maso Yamma kamar Zamfara, Kaduna, Sokoto, da Kebbi.
A bana an kashe daruruwan mutane ko kuma aka yi garkuwa da su a Katsina, wasu dubbai kuma aka tilastawa barin gidajensu.