By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Ribas a ranar Asabar ya dakatar da dokar hana fita na tsawon watanni 14 da aka sanya a jihar.
Mista Linus Obogo, wanda shine mataimakin babban sakataren yada labaran sa, ya sanar da dakatar da dokar hana fitar.
Idan za’a iya tunawa an dai kafa dokar ta-bacin ne a cikin watan Oktoban shekarar 2020, biyo bayan kazamin fashi da barnata dukiya a zanga-zangar #EndSARS.
A cewar sanarwar, yanzu ba a takaita zirga-zirga ba a fadin jihar a kowane lokaci.