Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ranar Alhamis ya gabatar da kudi naira miliyan 300,219,705,820 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da kuma amincewa da shi.
Kasafin kudin mai lakabin ‘Budget Of Consolidation and Renewed Focus’, ya kunshi kashe kudade akai-akai na N121,341,193,343.11 (40.4%) yayin da manyan aiyuka ya samu jimlar N178,878,512,477.49 (59.6%).
Kasafin kudin da aka gabatar ya nuna karin kashi 48.2 cikin 100 daga kasafin 2023.
Karanta nanDa Muku Muku Abba Ya Lashe Zabe A Kano-Ado Doguwa
Gwamnan ya danganta hakan ne da karin kudaden shiga daga cire tallafin da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Hakan na zuwa ne yayin da ya jaddada bukatar goyon bayan ‘yan majalisar don ciyar da jihar gaba da inganta rayuwar ‘yan kasa, inda ya bukaci a gaggauta aiwatar da kasafin kudin domin aiwatar da ayyuka masu tasiri a kan lokaci.
Da yake gabatar da kasafin kudin, gwamnan ya ce, “Mai girma shugaban majalisar wakilai, kasafin kudin 2024 an riga an tsara kasafin kudin 2024 kan hasashen samar da mai na ganga miliyan 1.78 a kowace rana.
Farashin mai na dalar Amurka 73.96 kowace ganga; canjin N700 zuwa dalar Amurka; ingantaccen matakin tara kudaden shiga a cikin Asusun Tarayya wanda ya taso daga cire tallafin mai; da ingantaccen tsarin tattara kudaden shiga na cikin gida.
A wani labarin kuma‘Yan Bindiga Sun Sace Amarya Da Limamin Wani Kauye A Kaduna
Gwamnati a yayin da take shirye-shiryen kasafin kudin ta dauki matakai wadanda suka hada da tabbatar da kammala ayyukan da ake gudanarwa, gabatar da sabbin ayyuka.
Kakakin majalisar, Babayu Mohammed Akuyam, a nasa jawabin ya baiwa bangaren zartaswar gwamnati tabbacin cewa majalisar za ta binciki kasafin kudin tare da tabbatar da gaggauta amincewa da kasafin kudin.