Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba da tabbacin bayar da karin goyon baya ga hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta jihar, domin ta zama jiha mafi kyawu a cikin shirin bayar da gudunmawar kiwon lafiya a Arewa, Tribune Online ta rawaito.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da babban sakataren hukumar bayar da gudunmawar lafiya ta jihar Yobe, Dakta Babagana Tijjani, ya ba shi katin shaida na hukumar.
KARANTA WANNAN: Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Murabus Din Jami’anta 25 Kan Abu 1
Buni ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.
“Gwamnati za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da ake da su tare da kaddamar da sababbi don tabbatar da ingantacciyar hanyar samar da kiwon lafiya a jihar.”
A cewar sakataren zartaswar, Dr Tijjani, jihar Yobe ta lashe kyautar Naira miliyan 30 da gidauniyar Bill and Melinda Gates ta bayar a matsayin jiha mafi kyau a shiyyar Arewa maso Gabas.
Ya ce sama da mutane 300,000 a sassa daban-daban suke jin daɗin hidimar hukumar lafiya ta jihar.
A cewarsa, an shigar da karin mutane 2,500 masu rauni a shirin don cin gajiyar lambar yabo ta Bill da Melinda Gates.
Ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar tana gudanar da shirye-shirye guda biyar wadanda suka hada da bangaren da suka ci gajiyar su 201,655 wanda ya kai kashi 96% na abin da ta sa a gaba.
“Muna da shirin Buni Equity Programm wanda ya kunshi masu cin gajiyar su kimanin 28,871, da kuma masu cin gajiyar guda 43,997 na
Asusun ba da tallafin kiwon lafiya na asali yayin da Gidauniyar Bill da Melinda Gates ke da masu cin gajiyar 2,500.”
Tijjani ya ci gaba da cewa jihar Yobe ita ce kadai jihar da ke da irin wannan nasarorin da ta samu lambar yabo.
Sakataren zartarwa ya sadaukar da lambar yabon ga Gwamna Buni, saboda jajircewar sa da kuma manufofin siyasar gwamnatinsa na samar da isasshiyar lafiya da rahusa ga al’ummar jihar Yobe.
A wani labarin kuma, Adamawa: SEC Ta Amince Da Karin Kasafin Kudin 2023 Na Naira Biliyan N39bn
Majalisar zartaswar jihar Adamawa, SEC, a zamanta na farko a ranar Alhamis, bayan kaddamar da sabbin kwamishinonin, ta amince da karin kudirin kasafin kudin jihar na Naira biliyan N39bn.
Za a aika da kudurin ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da kuma yiwuwar amincewa.