Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don ganin an ceto daliban jami’ar tarayya ta Gusau (FUGUS) da aka sace.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Suleiman Bala, ya fitar a Gusau ranar Alhamis.
Gwamnan ya kuma tsaya tsayin daka kan rashin tattaunawa da ‘yan bindiga, yana mai cewa dole ne su jefar da makamansu ko kuma su fuskanci fushin doka.
Karanta nanKotun Sojoji A Najeriya Ta Kama Babban Soja Da Laifin Satar Fiye Da Biliyan Daya
A nasa jawabin, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Mu’azu Abubakar, ya bayyana cewa har yanzu dalibai 12 na jami’ar da ma’aikatan gine-gine 9 suna tare da ‘yan fashin.
Ya bayyana cewa an ceto dalibai shida, sannan wasu tara suka tsere daga hannun ‘yan bindigar, inda suka bar sauran 21 da aka yi garkuwa da su.
Mu’azu ya ce hukumar jami’ar na ci gaba da tuntubar iyayen daliban da aka sace yayin da jami’an tsaro ke kara zage damtse wajen ganin an ceto su ba tare da samun wata matsala ba.
A wani labarin kumaAbinda Yasa Na Suma Ana Tsaka Da Tantanceni-Balarabe Musa
Mataimakin shugaban jami’ar ya bukaci iyaye da su kara hakuri da kuma yi musu addu’a Allah ya dawo da su lafiya.
Ya kuma bukaci daliban jami’ar da kada su shagaltu da karatunsu, inda ya tabbatar da cewa ana kokarin ganin jami’ar ta kasance mai tsaro wajen koyo. (NAN)