Gwamna Diri ya taya Musulmai murnar zagayowar ranar Mauludi
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya taya al’ummar musulmin jihar da ma fadin kasar nan murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Daniel Alabrah ya fitar, ya bayyana cewa bikin Eid-el-Maulud bikin soyayya ne kuma lokaci ne na yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah a kan hadin kai, tausayi da zaman lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu A Jahar Jigawa Ta Daure Wani Shekaru 10 Bayan Samunsa Da Laifin Fyade
Ya kuma umarci mabiya addinin Musulunci a jihar da su kasance masu kokarin zama masu rike da ‘yan uwansu, da nuna soyayya ta zahiri da tabbatar da zaman lafiya da sauran jama’a.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wannan lokaci mai albarka na gudanar da bukukuwan sallar Eid-el-Maulud, ina taya ’yan uwana musulmi murnar zagayowar wannan rana da kuma fadin Nijeriya.
“Yayin da kuke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad, kuma lokaci ne na yin tunani a kan manyan manufofinsa da koyarwarsa kan soyayya, hadin kai. tausayi da zaman lafiya.
“Ina kira ga masu bin addini da su nuna soyayya mai amfani, kishin kasa da tabbatar da zaman lafiya da sauran mutane. Ka’idodin kyakkyawar makwabtaka da kasancewa mai kula da ‘yan’uwa sun fi bayyana a lokacin kamar wannan.
“Bayelsa ta kasance gida ga kowa. Jiha ce da, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, kowa yana gudanar da addininsa cikin ’yanci ba tare da tsangwama ko bari ba. Kuma gwamnatinmu ta kasance da tsayin daka wajen ƙarfafa ’yancin yin ibada da tarayya.
“Yayinda zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba ya gabato, mu guji duk wani tashin hankali, mu ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A wani labarin kuma:Ina zubar da hawaye kan yanayin hanyoyin Najeriya – Umahi
Ministan ayyuka, Dave Umahi ya ce ya zubar da hawaye bayan ya bi ta wasu hanyoyin gwamnatin tarayya a yayin wani ziyarar aiki da ya yi a kwanakin baya.
Ya bayyana hanyoyin saye da sayarwa a matsayin babban kalubale ga babban burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.