Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bayar da umarnin sayen irin itatuwan bishiyoyi 500,000 domin dasawa wajen dakile illolin sauyin yanayi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Wannan dai na zuwa ne kasa da wata guda bayan da gwamnan ya bayyana sake farfado da dokar yaki da sare itatuwa a matsayin martani ga yawaitar ambaliyar ruwa da sauran illar sare itatuwa.
KARANTA WANNAN: Gwamnan PDP Ya Amince da Daukar Malamai Aiki
Da yake magana kan matakin dashen itatuwa 500,000 a fadin jihar, babban sakataren ma’aikatar muhalli, Cletus Hilkiah Gwotyel, ya ce gwamnan ya umurci ma’aikatar da ta sayo irin itatuwan shukar domin duba sare dazuzzuka.
Babban Sakataren, yayin da yake karbar bakuncin kwamitin kula da muhalli da raya albarkatun kasa na majalisar dokokin jihar Adamawa a ranar Juma’a, ya ce ma’aikatar tare da sassan fasaha guda hudu da daraktoci bakwai, tana da abubuwan da take bukata na dan adam domin gudanar da aikinta.
A nasa bangaren, kwamitin majalisar da ya kai ziyarar, ya ce a shirye yake don tunkarar matsalolin da ke kunno kai dangane da sauyin yanayi a jihar.
Shugaban kwamitin, Yohanna Jauro, wanda shi ne mamba mai wakiltar mazabar Mubi ta Kudu, ya ce saran bishiyu da aka yi a baya ya taimaka matuka wajen sauyin yanayi.
Ya ce lamarin na bukatar takamaimai matakan gyara kamar yadda gwamnan jihar ya ba da umarnin shuka itatuwa.
“Daya daga cikin ‘yan kwamitin Paul Samuel daga mazabar Mubi ta Arewa ya ce kwamitin zai bukaci tallafi daga ma’aikatar domin ci gaban jihar.
A wani labarin kuma, Wani Jigon PDP, Ya Caccaki DSS Kan Cigaba da Tsare Emefiele
Wani jigon jam’iyyar PDP, Injiniya Anslem Ijebor, ya caccaki ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefele yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sanya baki a ci gaba da tsare shi da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ke yi masa.
Ijebor duk da dan jam’iyyar PDP ne wanda ya zama abokin Peter Obi, a zaben shugaban kasa da ya gabata, bisa hujjar da aka yanke masa, ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.