Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa a ranar Alhamis ya yi ta’aziyyar rasuwar mutane uku da suka mutu a hatsarin mota kirar Toyota Hilux Van wanda take jigilar wasu ‘yan banga da ke cikin tawagar yakin neman zabensa zuwa yankin Gella Mubi ta Kudu da ke jihar.
Fintiri, a lokacin da yake zantawa da magoya bayansa a garin Gella dake yankin Mubi ta Kudu, ya ce ya damu matuka, kuma ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar PDP a wajen taron da su yi shiru na minti daya ga wadanda suka rasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kwara Abdulrazaq Ya Musanta Korar Ma’aikatan Gwamnati A Jihar
“Jam’iyyar tana jimamin mutuwar mutane uku da ke cikin tawagar kuma suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota,” in ji Fintiri.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa hatsarin ya afku ne a kusa da Fadamareke da ke karamar hukumar Hong mai tazarar kilomita 80 daga garin Mubi.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai shugaban ’yan banga, Bako Kaura; dan shugaban kungiyar ‘yan banga ta Fintiri/Farauta, Adamu Kaura; da wani ma’aikacin motar.
Wani mazaunin garin wanda ya zanta da wakilinmu, ya ce wurin da hatsarin ya faru ya yi kaurin suna wajen haddasa hadarurrukan hanya.
Ya bayyana cewa mazauna garin sun taimaka wajen zakulo gawarwakin mutane uku da suka hada da motocin dakon kaya kafin ayarin motocin Fintiri su isa wurin.
A makon da ya gabata ne dai gwamnan da kyar ya tsallake rijiya da baya, yayin da wata babbar mota da ta rasa yadda za ta yi, ta kutsa cikin ayarin motocinsa.
An garzaya da ‘yan sanda biyu da suka samu munanan raunuka zuwa asibitin kwararru na jihar domin yi musu magani.
A wani labarin kuma, Ba ka da kwanciyar hankali, kaje ka maida hankali kan inda Matar ka take — Atiku ga Oshiomhole
Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Atiku/Okowa ta ce ya kamata tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya mayar da hankali kan inda “matar sa ta ƙasar waje take.”
Kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su dauki Oshiomhole da muhimmanci saboda ba shi da kwanciyar hankali.
Yana mai da martani ne ga kalaman Oshiomhole inda ya bayyana jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin ‘maci amanar kasa’ kuma ‘dan saki’, wanda ba zai iya hada kan kasa ba.