Daga Uzairu Dauda Bunga
Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dada bayar da manyan mukamai da zasuyi aiki a gwamnatinsa a wa’adi na biyu.
Gwamnan ya nada mukamai guda tara da suka kunshi hukumar wasanni ta Kano Pillars da aka bawa Alhaji Sirajo Shu’aibu Yahaya a matsayin Shugaba, Injiniya Hadiza Ahmed Tukur Manajan daraktan kamfanin samar da hasken wutar lantarki na jahar Kano, Dr Usman Tijjani babban Sakataren hukumar kula da Asibitoci masu zaman kansu da Alhaji Uba Zubairu Shugaban kasuwar sabon gari ta Muhammadu Abubakar Rimi.
Sauran sune, Yahaya Adamu Garin Ali Shugaban samar da hanyoyin karkara da kayan aikin gona, Honorable Abubakar Zakari Muhammad Shugaban hukumar tallafin karo ilimi ta jahar Kano tare da Dr Yusuf Muhammad Sabo Shugaban hukumar kare hakkin masu saye da sayarwa
Sai kuma Ibrahim Salisu Bichi Shugaban hukumar samar da raba ruwan sha
da kuma Alhaji Abba Muhammad Bello Shugaban kasuwar kantin Kwari.
Cikin takardar da aka rabawa manema Labarai dauke da sa hannun babban Sakataren watsa Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar. Gwamnan da yake amincewa da nadin nasu, ya umarcesu da suyi aiki tukuru, sadaukar dakai da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Bayan ya tayasu murnar nadin nasu, Gwamna Ganduje ya bayyana musu cewa an zabo sune daga cikin dubun mutane Saboda irin gudumawar da suka bayar na jin kan bani Adama.
Sai ya kara da cewa “Ku dauki wadannan sabbin mukamai da aka baku a matsayin kalubale, ya rage naku yanzu, ku nuna mana cewa kun cancanci wadannan mukamai. Domin sauke nauyin da aka dora muku.”
Gwamna Ganduje, ya ummarcesu da suyi amfani da ilimin na’urar zamani wajen gudanar da ayyukansu.
“Duniyar yau, tana bukatar na’urar zamani domin gudanar da ingantacce da kuma sahihin aiki. Don haka ina ummartar dukkan wadanda aka nada da suyi amfani da tsarin, muna bukatar sakamako mai Inganci a kowanne lokaci cikin ofisoshinmu.” cewar gwamna Ganduje.