Gwamna Ganduje Ya Soke Filayen Ginin daya ruguje, Ya Mai dashi wurin ajiye Abun Hawa
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya soke filin da wani gini mai hawa uku ya ruguje a hanyar Beirut, kasuwar GSM.

KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NSCDC ta kama Masu Gadi 13 a Anambra
Ginin wanda ya ruguje a ranar Talata ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka jikkata.
Duk da cewa ba a iya tantance masu ginin ba, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), ta ce ba a gina ginin ba yadda ya kamata.
Sai dai a ziyarar da gwamnan jihar ya kai inda lamarin ya faru a ranar Laraba, ya ce, “Da farko dai wannan wurin ya kamata ya zama wurin ajiye motoci kawai. Ya yi ƙanƙanta don ginin shago.”
Ganduje ya bayar da umarnin a mayar da wurin zuwa wurin ajiye motoci, ya kuma kara da cewa an kafa wani kwamitin fasaha mai karfi da zai binciki musabbabin aukuwar wannan bala’i da gaggawa.
“Ya kamata mu sani cewa daga farko, kowane gini ya kamata a tsara shi da kuma kula da shi ta hanyar kwararru. A cikin mako guda wannan kwamiti ne kawai zai gabatar da rahotonsa kuma za mu yi aiki da shi yadda ya kamata,” inji shi.
Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su baiwa ma’aikatan da suke aikin tono tarkace hadin kai, inda ya kara da cewa bayan an tono tarkacen wurin yadda ya kamata, nan take gwamnati za ta fara samar da filin ajiye motoci da ya dace.
A wani labarin kuma:Da Ɗuminsa: Na magance yajin aikin ASUU a rana daya – Jonathan
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatin sa ta warware yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i tayi na tsawon watanni hudu a rana ɗaya.
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen bikin cika shekaru 70 na Mathew Hassan Hassan Kukah, Bishop na darikar Katolika na Sokoto, wanda cibiyar Kukah ta shirya.