By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Dakta Michael Ezeugwu Ajogwu, SAN, a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Enugu (ENSIEC), a karo na biyu, a dakin taro na EXCO, dake gidan gwamnati, Enugu.
Gwamna Ugwuanyi ya kuma rantsar da Dakta Greene Anike-Nweze a matsayin memba na ENSIEC a karo na biyu.
Dakta Ajogwu da Dakta Anike-Nweze an rantsar da su a matsayin shugaban hukumar zabe ta jihar ENSIEC da mamba bayan Gwamna Ugwuanyi ya sake nada su.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, Dakta Ajogwu a madadin sa da takwarorinsa, ya gode wa Gwamna Ugwuanyi bisa irin wannan karamci da ya yi musu ta hanyar ganin sun cancanci yin wa’adi na biyu bayan sun yi nasarar kammala wa’adinsu na farko na shekaru biyar.
Babban Lauyan Najeriya (SAN) ya yi wa gwamnan alkawarin cewa za su gudanar da ayyukansu cikin aminci da bin doka da kuma rantsuwar aiki.
A nasa jawabin, Gwamna Ugwuanyi ya taya su murna tare da yi musu fatan alheri a sabon wa’adinsu na aiki.
Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa sauran mambobin kungiyar ta ENSIEC bisa jajircewarsu da kuma kwazon da suka nuna na sauke nauyin da aka dora musu.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Simon Uchenna Ortuanya, mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Farfesa Malachy Okwueze, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Steve Oruruo, sakataren ENSIEC, Barista Chukwudi Amah, da sauran mambobin Hukumar sun shaida taron.
Kazalika yayin da babban sakatare na ma’aikatar shari’a da kuma mai shigar da kara na jihar Barista Victor Emeribe, ya rantsar da Dr. Ajogwu da kuma Dakta Anike-Nweze.
Comments 1