Gwamna Makinde Ya Buƙaci Baiwa Ƴan Siyasa Shekaru 6 A Duk Wa’adi
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayar da shawarar a yi wa ‘yan siyasa wa’adi daya na shekaru biyar ko shida.
Makinde ya ce ya kamata ‘yan siyasa su yi koyi da shugabancin kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) na wa’adi daya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zamana Shugaban APC Zai Kara Yawan Masoyan Jam’iyar-Ganduje
Ya na mai da martani ne ga shugaban PFN na kasa, Bishop Wale Oke na cewa shugabancin hukumar ba ya bada damar sake tsayawa takara karo na biyu.
Oke ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wurin bude taron kungiyar PFN ta kasa a Ibadan.
Sai dai da yake jawabi a wurin taron, Makinde ya ce ya kamata ‘yan siyasa su yi koyi da PFN, yana mai jaddada cewa shekaru hudu ba za su isa a cimma burin mutum ba.
A cewar Makinde: “A karon farko na ji cewa babu wa’adi na biyu a PFN. Wataƙila, muna bukatar mu koyi abubuwa ɗaya ko biyu daga wannan tsarin ga al’ummarmu.
“Ni mai goyon bayan tsarin wa’adi guda ne. Hasali ma bana son wani wa’adi na biyu kuma na ce wa ubannin imani shekaru hudu ba su isa ku yi duk abin da kuke so ku yi ba ya isa ku yi tasirin ku kuma ku bi hanyar ku.
“Idan muka sami damar tattauna wannan, ina ganin shekaru biyar ko shida na wa’adin mulki, watakila shekaru biyar, za su wadatar da yawancinmu mu yi duk abin da ya kamata mu yi.
A wani labarin kuma:Zamana Shugaban APC Zai Kara Yawan Masoyan Jam’iyar-Ganduje
Dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, Sanata Dino Melaye, ya yi alkawarin sake duba shari’ar korar ma’aikata a jihar cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Sanata Melaye, wanda ya bayyana shirinsa a Lokoja a lokacin da ya karbi bakuncin wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu sakamakon mummunan korar da aka yi wa ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi a fadin jihar ta Kogi, ya ba da tabbacin aniyarsa ta sake duba duk irin wadannan shari’o’in da fatan ganin an yi adalci ga wadanda abin ya shafa.