By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayar da umarnin dakatar da babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomin jihar, da al’amuran masarautu da raya karkara saboda jinkirin rashin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi a watan Nuwamba.
Umahi ya kuma bukaci kwamishinan kananan hukumomin jihar, harkokin masarautu da raya karkara, SSA da SA a kan kananan hukumomi da shugabannin kananan hukumomi 13 da su sauke nauyin daya rataya a wuyansu ta hanyar tabbatar da cewa an biya su albashin daya kamata daga yanzu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun sakataren gwamnatin jihar Dakta Kenneth Igwe a ranar Juma’a, wanda aka rabawa manema labarai kwafin sanarwar a ranar Asabar.
Sanarwar tace, “Gwamnan jihar Ebonyi, mai girma, Cif David Umahi, ya lura da jinkirin rashin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi na watan Nuwamba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “A bisa haka ne gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da babban sakatare na ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu da raya karkara da kuma Akanta JAAC na tsawon wata daya ba tare da biyan sh albashi ba.
Sanarwar ta kara da cewa rashin bin umarnin gwamnan zai janyo tsaikon takunkumai.