Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nesanta kansa daga shigar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar kara a kotu, inda ya ce babu wanda ya isa ya kira sunansa idan mutum ya fadi zabe mai zuwa.
Idan zaku iya tuna cewa wasu sassan kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Wike da wani jigo a jam’iyyar PDP, Newgent Ekamon, sun kai Atiku, Aminu Tambuwal da PDP kotu kan zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Najeriya Miliyan 160 Na Fuskantar Barazanar Kamuwa Da Cutar Zazzabin Shawara – WHO
Sai dai da yake jawabi a wajen kaddamar da ‘yan majalisar wakilai a Fatakwal a ranar Juma’a, Wike ya ce ya mayar da hankali ne wajen isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar Ribas.
Kalamansa: “Mutane sun kira ni cewa na kai karar Atiku Abubakar kotu.
“Ina so in bayyana cewa ban je kotu ba. Ina so in ce shi ne ‘yan Najeriya su sani. Na yi shiru. Na shagaltu da isar da ribar dimokuradiyya.”
“Idan sun fadi zabe, kada kowa ya kira sunana. Na fada wa dan takara. “Idan ina son zuwa kotu, da na je kotu a cikin makonni biyu da yin zaben”
“Kungiyar ‘yan takarar ce ke yin duk wadannan abubuwa. Bari duniya ta ji. Su ne suke shirya dukan waɗannan abubuwa, suna tunanin za su ɓata sunana. “Ya kamata mu yi magana game da cin zabe.”