Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya jajantawa Sanata Mohammed Ndume bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Ali Ndume, wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Yuli kuma tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Gwamnan a cikin sakon ta’aziyyar da ya sanya wa hannu mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Muhammed Onogwu a ranar Larabar nan, ya bayyana cewa marigayi Ndume kwararren shugaban al’umma ne, wanda ya yi wa al’ummarsa hidima a lokacin rayuwarsa.
Ya kuma bukaci Sanatan da daukacin ‘yan uwa da su yi hakurin jure rashin bisa yadda ya gudanar da rayuwa mai inganci tare da renon ‘ya’yan da nagartattu.
Hakazalika Bello ya mika sakon ta’aziyyarsa ga al’ummar mazabar Borno ta Kudu mai wakiltar mazabar Sanatan Borno ta kudu tare da addu’ar Allah ya jikan marigayi da hakurin jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.
(NAN)