Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Juma’a ya jagoranci rantsar da sakataren gwamnatin jihar Borno, da masu ba da shawara na musamman guda uku da kuma babban sakatare na ma’aikatan jihar Borno, Vanguard ta rawaito.
A wani biki da aka gudanar a dakin taro na kasa da kasa na sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri, babban alkalin jihar Borno, Kashim Zannah ne ya rantsar da sabbin wadanda aka nada.
KARANTA WANNAN: INEC, APC da Gwamna Alia, Sun Roki Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Wata Bukata
Da yake gabatar da jawabinsa bayan kammala rantsuwar, Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa, a aika masa da fayil-fayil da duk wata hanyar sadarwa ta gwamnati zuwa ga ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Zulum ya ce “Dukkan hanyoyin sadarwa zuwa ofishina kan yadda ake gudanar da harkokin gwamnati dole ne su bi ta ofishin sakataren gwamnatin jihar domin samun jagora, alkibla da shawarwari”.
Gwamnan ya yi kira ga wadanda aka nada da su cika burin gwamnati da al’ummar jihar Borno.
Sannan ya bukaci babban sakataren da ya tabbatar da cewa ba za a bari a bar aikin gwamnati ya dade ba.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa sabon sakataren gwamnatin Alhaji Bukar Tijani, ya kasance tsohon karamin ministan noma daga watan Yulin shekarar 2011 zuwa watan Satumbar 2013.
A wani labarin kuma, Wani Gwamna a Arewa Ya Tabbatar Da Nadin Manyan Sakatarori 36
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya amince da sake nada sabbin manyan sakatarori guda 36 na ma’aikatun jihar.
Gwamnan ya ce nadin nasu ya samo asali ne a bisa bajintar da suka yi, da nagartattun ayyuka da kuma jajircewarsu wajen biyan bukatun jihar.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Kamar yadda sanarwar ta kunsa, an sake nada manyan sakatarori 13 daga cikin 36, yayin da sauran 23 din suka kasance sabbin daraktoci da aka daukaka zuwa matsayin manyan sakatarori.