Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sanar da sakin karin zunzurutun kudi har Naira biliyan 1b domin kammala aikin sake gina kasuwar Monday Market dake Maiduguri, Tribune Online Ta rawaito.
Idan za’a iya tuna wa Jaridar Dimokuradiyya ta rahoto cewa Wata gobara ta tashi a kasuwar ta Monday Market a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2023 wadda ta kone sama da shaguna da kayayyaki sama 15,000 na miliyoyin Naira.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Yi Sabon Nadi A Gwamnatin Sa, Bayanai Sun Fito
Da yake magana yayin ziyarar duba kasuwar a ranar Litinin a Maiduguri domin tantance irin ci gaban da aka samu na sake gina kasuwar, Zulum ya ce sakin kudin Naira biliyan daya zai ba da damar kammala kasuwar cikin sauri nan da watan Satumba na 2023.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana sane da halin da ‘yan kasuwar ke fuskanta tun bayan rufe kasuwar watanni biyar da suka gabata.
A cewarsa, aikin ginin zai hada da gyaran kasuwar inda ‘yan kasuwa da dama suka rasa shagunansu.
“Saboda abubuwan da suka gabata, ina so in sanar da sakin wasu tsabar kudi Naira biliyan 1 don gaggauta kammala ayyukan”.
“Ina so in tabbatar muku (yan kasuwa da mutanen Maiduguri) cewa za mu kammala wannan aikin na sake ginawa nan ba da jimawa ba, insha Allahu.
“Ina sane da abubuwan da kuke fuskanta, amma ku tabbata nan da kwanaki 30 masu zuwa, mafi girman kwanaki 35 za mu kammala wannan aiki bi iznillah.
“Kasuwar Monday Market dake Maiduguri za’a sake bude ta ko kuma kafin ranar 10 ga watan Satumba insha Allahu,” in ji Zulum.
“Mun yanke shawarar sake fasalin kasuwar don ba da damar zirga-zirgar ababen hawa a ciki, mun sanya magudanun ruwa don kwararewar najasa da ruwan sama kyauta.
“Sakamakon gyare-gyaren, an rusa shaguna da dama. Domin saukar da wadanda suka rasa shaguna, muna gina karin adadin kananan shaguna.”
Ya roki Allah da rahamarsa marar iyaka da ya kawo karshen afkuwar bala’in gobara a kasuwar Maiduguri a nan gaba.
Gwamnan ya ba da shawarar kwamitin mambobin kasuwar da su kula sosai, yana mai cewa “bari in mika godiyata ga shugaban da mambobin wannan kwamiti (saboda kyakkyawan aikin da suke yi)”.
A wani labarin kuma, Dalilin Da Yasa Na Kawo Karshen Tallafin Man Fetur – Shugaba Tinubu
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bayyana dalilan da suka sanya ya kawo karshen tallafin man fetur
Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabin da ya yi a fadin kasar a ranar Litinin ya ce ana cusa kudaden ne a cikin manyan aljihu da manyan asusun ajiyar banki na wasu zababbun mutane
“A zahiri, Nijeriya ba za ta taba zama al’ummar da aka yi niyya ta zama ba, matukar irin wadannan kananan kungiyoyi masu karfi wadanda ba zababbu ba suna da tasiri sosai kan tattalin arzikinmu da siyasa