Gwamnan Arewa Ya Caccaki Buhari Kan Kashe Makudan Kudade Ga Matatun Man Najeriya
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule a ranar Alhamis ya soki yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kashe kudade a matatun man kasar.
Sule ya ce an kashe sama da dala biliyan 19 akansu amma babu wanda ke aiki, inda ya ce an yi amfani da kudin wajen gina matatar man Dangote a Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sowore Ya Caccaki Wike Da Gwamnonin G5 Kan Taro Da Tinubu
Gwamnatin tarayya ta mallaki matatun mai guda uku a Kaduna, Fatakwal (Rivers) da Warri (Delta) amma har yanzu babu wanda ya ke amfani.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television Sunrise Daily, Sule ya koka da yadda makudan kudaden da aka fitar ba su haifar da sakamakon da ake tsammani ba.
“A cikin shekaru takwas, shi (Buhari) ya kashe kudi fiye da dala biliyan 19 da Dangote ya kashe wajen gina matatar mai.
“Wannan ya ninka girman matatun mu uku sau daya da rabi. Daga bangaren gwamnati, ina ganin ba mu yi aiki mai kyau ba, ”in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa, yayin da matatun man ke da jimillar ganga 450,000 a kowace rana, kamfanin Dangote ya yi alfahari da 650,000.
Sule ya ce kamata ya yi gwamnatin da ta shude ta mayar da hankali wajen ganin an samu matatar mai guda daya ta yi aiki gadan-gadan maimakon kokarin gyara duka ukun.
A wani Labarin Kuma:Gobe ne za a fara jigilar Alhazan Jihar Taraba
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Taraba ta ce za a fara jigilar maniyyatan jihar zuwa kasar Saudiyya a gobe Asabar a filin jirgin sama na Yola da ke jihar Adamawa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Hamza Baban Muri ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Jalingo