Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River ya bi sahun masu neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023.
Gwamnan wanda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata, ya ce ya sanar da shugaban burin sa.
Ayade, wanda ya ce shugaba Buhari ya shawarce shi da ya kara tuntubar juna kafin ya bayyana, ya kara da cewa ya zo ne domin neman jagoranci na ruhi da na siyasa daga shugaban kasa kan wanda zai karbi ragamar mulki daga hannun sa ya zo 2023 domin ci gaba.
Ya ce batun tsaro, tattalin arziki, wutar lantarki da samar da aikin yi ne zai mayar da hankali wajen sanarwa, idan ya zama shugaban kasa.
Gwamnan wanda ya yi alkawarin maimaita abin da ya yi a jihar Cross River, ya bayyana cewa, idan har shugaban kasa ya kasance a shiyyar Kudu, a shirye yake ya dauki wannan kalubalen a matsayinsa na gwamna daya tilo a jam’iyyar APC a Kudu maso Kudu.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Orji Kalu tsohon gwamnan Jihar Abia ya fice daga sahun masu zawarcin Kujerar Shugaba Buhari a 2023.
Comments 1