Gwamnan Delta Oborevwori ya kori kwamishina da wasu
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya bada umarnin dakatar da kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Omoun Perez cikin gaggawa.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr. Kingsley Emu, ya ce gwamnan ya kuma umarci babban sakataren ma’aikatar, Bennett Agamah; Mataimakin Darakta, Injiniyan Aikin Noma, Oki Yintareke; da Babban Akanta, Gabriel Idiatacheko, ya ci gaba da tafiya hutun har sai an samu sanarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da duminsa: Kotun koli ta tabbatar da zaben Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa
Ya bayyana cewa matakan sun zama wajibi ne biyo bayan nazarin aiwatar da aikin Greenhouse da ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jihar ta yi.
Sannan ta ce an dauki matakin ne sakamakon rahoton wucin gadi na kwamitin da kuma samun damar samun bayanai ba tare da wani cikas ba a lokacin gudanar da bincike.
“Oborevwori ya kafa wani kwamiti na mutum bakwai karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Dr. Kingsley Emu, don bincikar da’awar da kuma fahimtar rashin gaskiya da ke da alaka da gudanar da shirin ta ma’aikatar,” in ji shi.
Ya ce matakin da gwamnati ta dauka ba wai wani zato ne na laifi ba, sai dai matakin da ya dace don tabbatar da tsarkin tsarin binciken da aka riga aka kafa wanda shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken ba tare da wani tasiri ko son zuciya ba.
A wani labarin kuma:Ka Kori ministocin da ba sa aiki – Kakakin Majalisa Abbas ga Tinubu
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya kori ‘yan majalisar da ba sa aiki.
Abbas, wanda ya bayyana hakan a yayin da ake ci gaba da zaman majalisar a ranar Talata, ya kuma bayar da shawarar daukar sabbin dabarun magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar.