Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa bangaren kiwon lafiya na jihar na bukatar sabbin likitoci sama da 200 da za su iya kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar.
Obaseki ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin sabbin shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta (ARD) a jihar da suka kai ziyarar ban girma a ofishinsa.
“Muna buƙatar sabbin likitoci fiye da 200 a cikin tsarin kiwon lafiyar mu, waɗanda za su kasance a cikin al’umma don kula da Cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko a fadin jihar,” in ji shi.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan yadda za a samar da karin likitoci ta hanyar karfafa tsarin ilimi da ba da ingantaccen ilimi don samar da karin likitoci ga jihar.
Obaseki ya yi kira ga hadin gwiwar likitocin don ci gaba da sauye-sauye a fannin kiwon lafiya, tare da ba da tabbacin samar da tsayayyen tsari da daidaito don isar da ingantaccen aikin kula da lafiyar.
Ya ce gwamnatinsa na magance matsalar karancin kayan aikin likitanci na zamani, gurbacewar kayayyakin kiwon lafiya, rashin isassun ma’aikata da karancin kudade da ke da alaka da bangaren a baya.