Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON ya taya Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya NSCIA murnar bikin cikar sa shekaru 67 a duniya.
Bayanan hakan sun fito ne ta cikin sanarwar ta bakin Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe Ismaila Uba Misilli
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Gombe Ta Bukaci Mutane Su Rungumi Noma, Yayin Rabon Tallafin FG
Gwamna Inuwa ya bayyana Sultan a matsayin madogaran zaman lafiya da hadin kai, wanda matsayinsa na jagorar ruhi ga musulmi a fadin Najeriya ya samar da zaman lafiya mara misaltuwa a tsakanin al’ummar musulmi da ma bayansa, ya ketare iyaka ya taba rayuwar mutane da dama.
Ya yi nuni da cewa sadaukarwar da Sarkin Musulmi ya yi na samar da zaman lafiya har yanzu yana da matukar muhimmanci wajen jagorantar al’umma da shugabanninta wajen samar da ingantaccen shugabanci da walwala.
“A matsayinsa na mai kula da al’adunmu, Mai Martaba Sarkin ya jajirce wajen ganin an samu hadin kai da hakuri da juna. Yunkurinsa ya samar da hadin kai, daidaiton addini, da zaman lafiya tare da karfafa ginshikin al’ummarmu”.
Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ya bukaci Shugaban NSCIA da ya ci gaba da yin amfani da daukakar sarautarsa da gagarumin tasirinsa wajen inganta zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai kyau, ba kawai a cikin Halifanci ba, har ma a fadin kasa da ma sauran kasashen duniya.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya kara wa Shugaban Musuluncin Nijeriya shekaru masu yawa cikin koshin lafiya domin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na ban mamaki ga al’umma, kasa da kuma bil’adama.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Za Ta Biya N700m Ga Daliban BUK, N854 Don Auren Zawarawa
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 700 don biyan kudin makarantar ‘yan asalin Kano 7,000 da ke karatu a Jami’ar Bayero Kano.
Bugu da kari, an ware Naira miliyan 854 don shirin bikin Auren Zaurawa a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a shafinsa na X da aka tabbatar, wanda aka fi sani da Twitter.
Gwamnan ya ce amincewa da Naira miliyan 700 ga daliban Kano a makarantar BUK an yi shi ne a yayin taron majalisar zartarwa ta Jiha a ranar Larabar da ta gabata kan matsalar tattalin arzikin da kasar nan ke fama da shi.