Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gana da shugabannin kungiyar al’adun Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, domin tattaunawa da kuma magance matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar.
Taron wanda ya gudana a gidan shugaban kungiyar na kasa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya mayar da hankali ne kan neman goyon bayan kungiyar al’adun gargajiya wajen yakar al’amuran da suka shafi garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran miyagun laifuka a jihar.
Karanta nanJam’iyar PDP A Jahar Bayelsa Ta Gargadi Ganduje Akan Zuwa Rumfunan Zabe
Sule ya jaddada bukatar hada kai da kungiyar da sauran kungiyoyin Fulani a jihar, ganin yadda ake yawan samun wasu ’yan kabilar Fulani wajen kai hare-hare daban-daban, inda ya ce wasu al’amura da dama na faruwa ne daga mutanen waje da suka kutsa kai cikin jihar, suna haddasa barna.
Gwamnan ya bukaci ‘yan banga na kungiyar Fulani da su taimaka wa jami’an tsaro wajen ganowa tare da dakile hare-haren da wasu mutane daga waje suke yi a jihar.
Duk lokacin da aka yi garkuwa da mutane sai kaga an samu fulani da hannu a ciki,don haka ne na ga ya dace in tsaya a nan in yi magana da shugabannin Fulani kan bukatar ganin baki ba su shigo cikin jiharmu don yin ta’addanci ba.
Al’ummar Fulani a Jihar Nasarawa masu son zaman lafiya ne, don haka ya kamata mu yi duk mai yiwuwa don ganin cewa wasu ba su shigo cikin Jiharmu don aiwatar da miyagun ayyuka ba.
A wani labarin kumaKasar Saudiya Za Ta Saka Hannun Jari Akan Matatun Man Nijeriya
Da yake mayar da martani, Alhaji Bodejo ya yaba wa gwamnan bisa shirinsa na kawo kungiyoyin al’adu da addinai daban-daban na jihar kan teburin tattaunawa.
Ya kuma ba da tabbacin kungiyar ta kuduri aniyar hada kai da kungiyoyi da hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro da ake fama da su a kasar nan.