Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya amince da sakin Naira miliyan 100 ga kungiyar masu kamun kifi ta jihar Kebbi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Dabbobi da masunta, Aminu Garba Dandiga ya rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singer Dake Jihar Kano
Sanarwar ta ce, matakin da Gwamnan ya dauka ya yi daidai da kudurinsa na bunkasa noman kifi tare da karfafawa masunta a jihar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, akalla mambobin kungiyar 2,000 ne za su ci gajiyar shirin rancen. wanda Gwamnan ya yi alkawari a lokacin da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi kwanan nan.
A WANI LABARIN KUMA: Da Ɗumi-Ɗumi: An naɗa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ekiti
Ƴan majalisar Dokokin Jihar Ekiti sun zabi tsohon shugaban ‘yan kasuwar gwamnati Gboyega Aribisogan a matsayin sabon shugaban majalisar.
Aribisogan, wanda ya fito daga Ijesha-Isu a karamar hukumar Ikole, an rantsar da shi ne a zaman majalisar a ranar Talata wanda magatakardar majalisar, Mista Tola Esan Yayi.
Kujerar majalisa ta daya ta zama babu kowa bayan rasuwar kakakin majalisar Funminiyi Afuye bayan bugun zuciya.