Gwamnan Cross River Ben Ayade a ranar Talata ya kara wa’adin ritayar malaman makarata da shekaru biyar a jihar.
Gwamnan ya yanke wannan shawarar ne yayin wata ziyarar ban girma da kungiyar malamai ta Najeriya ta kai a ofishin gwamnan dake Calabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zabe: INEC Ta Dakatar da Wani Kwamishinan Zabe
Ayade ya kuma dage takunkumin karin girma ga malamai a jihar.
Ayade ya ce, “Malamai su ne lamirin al’umma, su ne masu tsara shugabannin gobe. Don haka, a gare mu a Cross River, malamai sun cancanci jin daɗin rayuwa.
“Don haka, an tsawaita shekarun ritayar malamai da shekaru biyar. An kuma dage takunkumin kara girma. Hakazalika, duk malaman da suka samu karin girma daga yanzu za su fara samun albashin da ya dace da mukamansu.”
Gwamnan ya bayyana cewa a cikin shekaru takwas na gwamnatin sa, ya inganta jin dadin malamai, ciki har da biyan albashin su cikin gaggawa, sannan ya yi alkawarin wanke duk wasu matsalolin da suka shafe su kafin ya bar aiki.
Shugaban kungiyar NUT reshen Cross River, Gregory Olayi, a baya ya bayyana gwamnan a matsayin aboki na malamai kuma ya ce sun yi godiya da ya samu lokacin karbar bakuncinsu.
Shima a nasa jawabin, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin ilimi, Kwamared Castro Nzama, ya ce malaman sun zo ne domin nuna godiya ga gwamna Ayade a bisa kyautatawa da manufofinsa na tallafawa malamai.
A wani labarin kuma, Shugaban Amurka Biden zai karbi bakuncin Firaministan Ireland
Shugaban Amurka, Joe Biden, a ranar Juma’a zai karbi bakuncin Firaministan Ireland, Leo Varadkar, a fadar White House, don taron gargajiya na St. Patrick’s Day, in ji sanarwar Amurka, gabanin ziyarar Biden a Ireland a wata mai zuwa.
Biden, wanda tushensa na Irish ne, ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai yi balaguro zuwa Ireland da Arewacin Ireland a wannan makon, don bikin cika shekaru 25 na yarjejeniyar Good Friday da Amurka ta kulla.