Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce daukar nauyin mutane su yi “karya da fadin rashin kunya” a kansa ba zai sa a cire shi daga mukamin minista ba.
Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara ne ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani kan zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar Zamfara ke yi masa.
Matawalle yayi gwamna tsakanin 2019-2023,ya sha kaye a takarar neman wa’adi na biyu a watan Maris a hannun Mista Dauda na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).
Karanta nanFiye Da Mutum Miliyan Daya Ne Za Su Yi Zabe A Jahar Bayelsa-INEC
Gwamnatin Zamfara ta zargi Matawalle da almubazzaranci da biliyoyin Naira na aikin filin jirgin saman jihar.
An kuma zarge shi da ba wa ma’aikatar kananan hukumomi umarnin cire Naira biliyan 1 daga asusun hadin gwiwa na kananan hukumomin a ranar 25 ga Oktoba, 2021, tare da biyan Naira miliyan 825 ga ‘yan kwangilar ba tare da wani bayani ba.
Sai dai da yake magana a wata hira da DCL Hausa, Matawalle ya zargi Lawal da daukar nauyin karya a kansa.
Ya ce kalubalen da ake fuskanta a jihar ba daga gwamnatin sa suka fara ba.
Ya ce akan maganar hanyar filin jirgin, bayan Dauda ya zama gwamna, ya yaudari jama’a da cewa zai gyara hanyar filin jirgin, sai kawai ya dauki buldoza a can ya kwashe hanyar da muka riga muka yi yace.
Ya yi haka ne don ya wulakanta ni kuma ya ce Matawalle ba ya aiki a jihar. Haka ya yi da Ruga. Mun yi komai, kuma mun zuba kudi amma ya lalata Ruga.
Ya kamata ya sani ba wai ya yi min haka ba amma ya yaudari mutanen Zamfara. Ya kuma damfari kansa saboda ya sha alwashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Zamfara.
A wani labarin kumaGwamnatin Tarayya Ta Kwaso Bakin Haure 161 ‘Yan Najeriya Da Suka Makale a Libya
Daya daga cikin titin filin jirgin sama, an kashe sama da Naira biliyan 4 amma ya fito yana karyar komai. Ya kuma lalata mana ayyukan more rayuwa a jihar don kawai ya fito ya yi min karya.
Na ji abin da ya ce game da ilimin jihar. Ina da takardun amma ya ki fahimta saboda ya makance yana kokarin wulakanta ni.
Daukar nauyin mutane don yin karya da faɗin abubuwan da ba su dace ba game da ni ba zai sa a cire ni a matsayin minista ba.