Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ce zai gyara tsarin Almajiri a yankin arewacin Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wata cibiyar siyasa mai zaman kanta, Chatham House a birnin Landan na kasar Ingila a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ban Taba Fadi Zabe Ba – Tinubu Ya Mayar wa Babachir Lawal Martani
A yayin da yake magana kan yadda gwamnatinsa za ta halarta domin samar wa matasan Najeriya masu hazaka idan ya lashe zaben shugaban kasa a 2023, Tinubu, ya ce za a samu rancen dalibai kuma za a samar da ingantacciyar hanya ga matasa don bunkasa fasahar.
Ko da yake tsohon gwamnan na Legas bai fayyace yadda zai cimma hakan ba amma ya yi fariya da cewa ya yi nasarar mayar da rancen kudade da dama zuwa kadarori a lokacin da yake mulkin Legas.
“Za a samu lamunin dalibai na Najeriya. Za mu gyara tsarin Almajirai. Matasa za su iya bunkasa harshen fasaha da kansu,” in ji Tinubu.
Almajiri yana nufin tsarin ilimin addinin Musulunci da ake yi a arewacin Najeriya inda yara maza da matasa suke barin jin daɗin iyayensu don neman ilimin addinin Musulunci.
Sai dai shirin almajiran ya sha samun suka sosai ganin yadda wadannan matasa mazan ake ganin su a kan titunan garuruwan arewacin Najeriyar suna zubar da sharar motoci, cibiyoyin ATM, otal-otal, gidajen karuwai, da ma wuraren ibada don yin bara.
Yawancinsu an mayar da su ‘yan amshin shata a hannun ’yan siyasa da ke amfani da su wajen biyan bukatar son kai don cutar da al’ummar Najeriya.
A wani labarin kuma, Bukukuwan Karshen Shekara: Hukumar NSCDC Ta Tura Jami’ai Sama Da 2,000 Kaduna
A ranar Litinin ne Hukumar Tsaron Fararan hula da kaddarorin Gwamnati ta kasa wato (NSCDC) reshen Jihar Kaduna, ta ce za ta tura sama da jami’ai ta 2000 zuwa wurare daban-daban, a cikin kananan hukumomi 23 dake fadin jihar a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSC Badamasi Babangida a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin ya bayyana cewa jami’an da za a tura za su kare kadarorin Gwamnatin a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.