Gwamnati tace ba zata amince waɗanda suka yi karatu a Burtaniya suyi aiki a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta maida martani kan kalaman da ta yi tun farko da ke nuni da cewa an amince da lauyoyin Ingila da Birtaniya su yi aiki a Najeriya.
Ministar ciniki da zuba jari ta Najeriya Doris Uzoka-Anite, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa lauyoyin da Birtaniya ta horar za su iya yin aiki a Najeriya, biyo bayan wata yarjejeniya ta habaka kasuwanci da zuba jari da Najeriya da Birtaniya suka sanya wa hannu a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gaskiyar abin da ya faru da Jarumar fim Maryam CTV
Sai dai, bayan sukar da suka yi masa, musamman kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, Uzoka-Anite ta janye kalamanta na farko.
A cikin jerin rubuce-rubucen da ta wallafa a shafinta na X, Uzoka-Anite ta ce: “A safiyar yau ne Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai nisa da kasar Burtaniya domin habaka kasuwanci da zuba jari.
“Abin takaici, rahotonmu na farko ya nuna kuskuren cewa Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da ta baiwa lauyoyin da ke da lasisi a Burtaniya damar gudanar da aiki a Najeriya. Muna so mu bayyana cewa babu wani tanadi ko yarjejeniya..”
Ministan ya bayyana cewa Najeriya ba ta da yarjejeniyar amincewa da juna da Birtaniya kuma ba ta yi wani alkawari a karkashin yarjejeniyar fahimtar juna ba ko kuma a wasu wurare na ba da damar lauyoyin da ke da lasisin Burtaniya su yi aiki a Najeriya.
“Kamar yadda yake a halin yanzu, lauyoyi masu lasisi daga kasashen waje (ciki har da wadanda ke da lasisi a Burtaniya) ba za su iya yin aiki a Najeriya ba, kamar yadda aka bayyana a cikin MoU.
Ta kara da cewa “Mun fahimci cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shari’a a Najeriya da Burtaniya, kuma hakan ya bayyana a cikin yarjejeniyar MoU.”
Ku tuna cewa Shugaban NBA, Yakubu Maikyau, ya yi Allah wadai da batun yarjejeniyar a wata sanarwa a ranar Talata, inda ya bayyana cewa furucin da aka yiwa Ministan abin dariya ne, rashin kishin kasa, da rashin sani.
A wani labarin kuma:Jami’an tsaro sun kashe wani abokin Marafa, gwamnatin jihar Zamfara ta ba da umarnin gudanar da bincike
Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu.
Rahotanni sun ce shugaban jam’iyyar ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba.