Gwamna Dauda Lawal ya kafa dokar ta baci kan harkokin ilimi a jihar Zamfara.
A wani jawabi da gwamnan ya yi a fadin jihar a ranar Talata, ya ce bangaren ilimi da aka yi watsi da su a Zamfara ya shafi dukkan matakai tun daga firamare har zuwa manyan makarantu, da rashin muhallin karatu da ma’aikata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce kafa dokar ta-baci kan ilimi ya yi daidai da alkawarin yakin neman zabe na gwamna Lawal.
Karanta nanYa Kamata ‘Yan Nijeriya Su Gwada Shugabancin Inyamuri-Wabara
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar na cika alkawarin da ta dauka na yiwa fannin ilimi garambawul, wanda kusan ya durkushe.
Sanarwar ta kara da cewa a wani sako da aka watsa yau, Gwamna Dauda Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a fadin jihar Zamfara.
Hakan ya yi daidai da tsarin yakin neman zabensa, inda ya yi wa al’ummar Zamfara alkawarin aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin gyara fannin ilimi, ginawa da gyara makarantun gwamnati, samar da isassun kayan aikin ilimi, da horar da ma’aikatan da ake da su.
Saboda haka, gwamnatin Dauda Lawal ta fara bayar da agajin gaggawa kamar horar da dukkan malamai da manajojin ilimi za su sami horo na musamman.
Don tabbatar da mafi karancin ingancin ilimi, gwamnati ta dakatar da lasisin masu ba da ilimi masu zaman kansu a jihar. Wannan yana tabbatar da cewa makarantu masu zaman kansu sun cika ka’idojin da ake buƙata don samar da ingantaccen ilimi.
Gwamnatin Jiha ta biya Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) kudin ga duk ‘yan makarantar Zamfara da suka zana jarrabawar 2023. Hakazalika an kuma karbo satifiket na wadanda suka zana jarabawar NECO na 2019 tare da raba wa daliban.
Za a fitar da sakamakon jarabawar NECO da aka yi a shekarar 2020, 2021, da 2022 ga dalibai kafin karshen watan nan. A baya hukumar NECO ta hana sakamakon zaben saboda rashin biyansu da gwamnatin da ta gabata ta yi.
A wani labarin kumaGwamanatin Katsina Ta Ware Biliyan 17 Domin Samar Da Ruwan Sha A Fadin Jahar
Gwamna Lawal ya biya kudin karatu da alawus-alawus na dalibai a kasashe daban-daban da suka hada da Sudan, Cyprus, da Indiya. Hakan ya tabbatar da cewa za su ci gaba da karatunsu ba tare da tsangwama ba saboda basussukan da gwamnatin da ta gabata ta ci.
Gwamnati ta kuduri aniyar canza labarin rashin aikin yi akai-akai. Zamfara za ta ci gaba a kowane fanni. Wannan shine farkon aikin cetonmu.