Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta dakatar da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire a jihar sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka yi.
Ku tuna cewa Vanguard ta ruwaito cewa NLC da TUC sun fara yajin aikin a ranar Talata da tsakar dare a fadin kasar nan.
Karanta nanYajin Aiki-TCN Ta Karyata Batun Dauke Wuta A Fadin Nijeriya
A ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, 2023 ne aka shirya gudanar da jarabawar, amma yanzu an dage jarabawar har abada.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar Ilimi ta Jiha, ta dakatar da Jarrabawar cancantar Sakandire ta 2023 (SSCE) da aka shirya gudanarwa a yau, Talata, 14 ga Nuwamba, 2023, har sai an samu sanarwa.”
Sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru, ta yi kira ga dalibai da iyaye/masu kulawa da su jure duk wata matsala da dakatarwar ta haifar.
Hakazalika, bankuna, asibitoci, da sauran wuraren taruwar jama’a a jihar, yajin aikin ya shafa.
A wani labarin kumaRundunar Sojoji Ta Yi Gargadi Akan Shafukan Daukar Aiki Na Jabu
Rundunar Sojan Najeriya ta bayyana rashin jin dadin ta game da yadda ake ta yada labaran bogi na daukar ma’aikata ta yanar gizo, musamman dangane da tashar daukar ma’aikata ta Sojojin Najeriya kai tsaye (DSS) na shekarar 2023.
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta gargadi jama’a game da fadawa tarkon ‘yan damfar
Ya ce Rundunar Sojin Najeriya na son bayyana cewa wallafar karya ta yanar gizo wani shiri ne na yaudara da wasu marasa kishin kasa suke yi domin yaudarar jama’
La’akari da illar da wannan wallafe-wallafen na jabu na yanar gizo za su iya yi ga tunanin masu son zama ‘yan takara da sauran jama’a, yana da mahimmanci a fayyace cewa karya ta hanyar Intanet Direct Short Service Portal 2023, zamba ce kuma ya kamata a kauce masaa.a.