Ministan makamashin Kasar Austaraliya Chris Bowen yayi kira ga al’umma garin Kudancin Wales da suka haɗa da garin sdyney birnin mafi girma a kasar da su rinka kashe wutar lantarki saboda rage kalubalen wutar lantarki da kasar ke fuskanta.
Wannan kiran na zuwa ne a dai dai lokacin aka rufe babbar tashar da ke samar da wutar lantarki ta kasar saboda da ƙaruwar farashin wutar.
Mr Bowen ya bukaci al’umma da ke zaune a garin da su rage yawan amfanin da wutar lantarki.
Rayhaan Rediyo ta rawaito cewa kasar Austaraliya wanda na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wurin fitar da sinadarin Coal da iskar gas a fadin duniya, ta faɗa cikin kalubalen karamci wutar lantarki tun watan da ya gabata.
Rahotanni sun nuna cewa kashi uku na wutar lantarkin ƙasar ana samar da shi ne ta hanyar makamashi Coal.
To sai dai a yan makwaninan, kasar Austaraliya na fuskantar karamci Samar da coal , dalili da tashin farashin makamashi a fadin duniya.