- Gwamnan Benue, Rev. Uba Hyacinth Alia, a ranar Juma’a, ya lissafa kadarorin da zai kwato daga hannun tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom
- Tun da farko gwamnan ya kafa kwamitin kwato kadarorin gwamnati da tsohon gwamnan ya sace
- Kwanaki kadan bayan da gwamnatin jihar ta sanar da kafa kwamitin, Ortom da mataimakinsa Abounu, sun shigar da kara a gaban kotu domin hana kwamitin da gwamnati daukar duk wani mataki
Gwamnan jihar Benue, Rev. Uba Hyacinth Alia, a ranar Juma’a, ya lissafa kadarorin da zai kwato daga hannun tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom, da mambobin gwamnatinsa.
Gwamna Alia ya lissafa wasu kadarorin da suka hadar da filaye mallakar gwamnati da motoci da gidaje da kayan daki da sauran injuna yayin da yake kaddamar da mambobin kwamitin kadarorin gwamnatin jihar da na kananan hukumomi a tsohon dakin liyafa na gidan gwamnati.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Filato Ya Yi Wasu Sabbin Nade-Nade, Ya Kuma Kafa Wani Kwamiti
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa tun da farko gwamnan ya kafa kwamitin kwato kadarorin gwamnati da aka sace tare da tsohon babban sakatare, Hingah Biem a matsayin shugaba.
Kwanaki kadan bayan da gwamnatin jihar ta sanar da kafa kwamitin, Ortom da mataimakinsa, Benson Abounu, sun shigar da kara a gaban kotu domin hana kwamitin da gwamnati daukar duk wani mataki na kwato kadarorin.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, wakilinmu ya kasa tantance ko an sanya karar zuwa ga alkali.
Yayin kaddamar da kwamitin a jiya, gwamnan ya bukaci mambobin kungiyar da shugaban kungiyar da su kwato dukkan kadarorin gwamnatin jihar da tsohuwar gwamnatin Ortom ta wawure ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, “Ba wai a ci zarafin kowa ko manya ba ne, amma abin da ya dace a yi shi ne a yi lissafin duk wasu kadarorin gwamnati.
A yayin da yake bayyana cewa ya sha samun zarge-zargen sauya sheka, cin zarafi da satar dukiyar gwamnati kai tsaye.
Gwamnan ya ce, “Ya dace kwamitin ya kuma tantance dukkan ayyukan kadarorin gwamnati da aka yi tsakanin 1 ga watan Maris zuwa 29 ga Mayun 2023, MDAs na gwamnati daban-daban ba tare da bin ka’ida ba.
Ya dage cewa kundin tsarin mulkin kwamitocin ya zama dole saboda dimbin motoci da aka gani tare da jami’an gwamnatin da suka shude amma ba a gansu ba.
Shugaban kwamitin, Hinga Biem, ya yi alkawarin cewa ba za su bai wa gwamnati da al’ummar jihar kunya ba wajen gudanar da ayyukansu.
A wani labarin kuma, Wata Ambaliyar Ruwa Ta Rushe Gidajen Da Dama A FCT
Ambaliyar ruwa ta lakume gidaje da dama a fitaccen rukunin gidaje na Trademore Estate da ke Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.
Ambaliyar ta kuma lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a safiyar ranar Juma’ar nan.