Gwamnatin jihar Benue ta ce ta kuduri aniyar hada kai da masu zuba jari da ke neman gano dimbin albarkatun ma’adinai a jihar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kwamishinan filaye, safiyo da ma’adanai, Mista Bernard Unenge ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Lahadin nan a Makurdi.
Ya ce Benue na da kusan dukkan albarkatun ma’adanai da ake samu a ko’ina a cikin kasar nan.
KU KARANTA KUMA Al’ummar Jihar Benue Sun Yi Watsi Da Mukaman Da APC Ta Basu
“Daga binciken da muka yi, muna iya fada muku cikin kwarin gwiwa cewa akwai dimbin ma’adanai daban-daban a jihar,” in ji Unenga.
Ya ce duk da cewa batun ma’adinai na hannun Gwamnatin Tarayya, jihar za ta hada kai da masu zuba jari don yin amfani da albarkatun.
“Jihar Benuwai na daya daga cikin jihohin kasar nan da ke da albarkar ma’adanai masu yawa.
“Muna da kusan dukkan ma’adanai da ake samu a Najeriya, tun daga Barite, Gypsum, Zinare, Lead, da duwatsu masu daraja.
A Wani Labarin Kuma Borno Ta Sami Rahoton Cin Zarafin Mata Guda 700 A Cikin Shekara Guda
Gwamnatin jihar Borno ta ce an samu bullar rahotan cin zarafin Mata guda 700 a cikin shekara guda a fadin kananan hukumomin uku na jihar.
Kwamishiniyar harkokin mata Hajiya Zuwaira Gambo ce ta bayyana hakan ga jaridar Daily trust a wajen horon kwanaki uku kan daidaiton jinsi da bayar da rahoto ga mata ‘yan jarida a jihar Borno.