By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Borno tace za ta rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira dake cikin Maiduguri, zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati a karshen wata ganawar sirri da yayi da Shugaba Muhammadu Buhari, a Abuja ranar Juma’a.
Yace an yanke shawarar rufe sansanonin dake Maiduguri ne sakamakon ci gaban da aka samu a yanayin tsaro a jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe sansanin don baiwa wadanda suka rasa muhallinsu damar komawa gidajen kakanninsu.inda ya kara da cewa”Na zo ne don yi wa shugaban kasa bayani kan kokarin da gwamnatin jihar Borno ta yi wajen tabbatar da dawo da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan, ya kammala shirye -shiryen dawo da mutanen da suka rasa muhallansu zuwa makwabtan Nijar da Jamhuriyar Kamaru, tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Agaji ta Tarayya.”Bugu da kari, a ranar 27 ga watan Nuwamba, gwamnatin jihar Borno zata tabbatar da sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar dake zaune a lardin Diffa na Nijar zuwa karamar hukumar Malumfatari, ta jihar Borno inda bamu da yawan mutane saboda tashin hankalin,” in ji shi.
Kazalika yace, “Don haka, sojojin Najeriya suna bayar da duk tallafin da ake buƙata ga gwamnatin jihar Borno.” Ina farin cikin sanar da ku kuma cewa Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Adm. Awwal Gambo, ya tabbatar da dawowar Sojan Ruwa. Base zuwa Baga a watan daya gabata. ”