Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da Naira biliyan 1.3 domin biyan bashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar da suka yi ritaya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arzikin jihar Muhammad Gambo Magaji ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jihar.
KARANTA HAKANAN Martanin Gwamntin Gombe Bayan Zarginta Da kama Dan Jarida
Ya ce gwamnan ya kuma amince da kashe Naira biliyan 1.7 domin biyan bashin da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2017 suke bi.
“Biyan bashin ma’aikatan da suka yi ritaya da suke daga cikin kudaden garatuti da wannan gwamnati ta lakume Naira biliyan 7.9. A baya Gwamna Yahaya ya biya bashin kudaden garaturin wadanda suka yi ritaya a jihar a shekarun 2014, 2015 da 2016 da yanzu na 2017,” inji shi.
A cewarsa, ma’aikatan kananan hukumomin da suka yi ritaya an biya su kyauta ta karshe a shekarar 2011.
Har ila yau, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Dasuki Jalo Waziri, ya ce gwamnan ya amince da karin girma ga ma’aikatan kananan hukumomi 26,085 a fadin kananan hukumomi goma sha daya na jihar nan take.
Ya bayar da wannan aiki a matsayin ma’aikatan kananan hukumomi 6,738, malamai 16,739 daga ma’aikatan ilimi da kuma ma’aikatan lafiya 2,608 daga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na kananan hukumomi 11.
Dasuki ya bayyana cewa karo na karshe da aka kara wa malamai karin girma a jihar shi ne a shekarar 2009 yayin da karin girma tare da tallafin kudi aka fara aiwatar da shi a shekarar 2014.
A Wani Labarin Kuma Alwashin Janairu: Wike Ya Jagoranci G5 Wajen Bayyana Sunan Dan Takarar Shugaban Kasa
Gwamnoni biyar, ‘ya’yan jam’iyyar PDP tsagin G5, sun kasa bayyana sunan dan takararsu na shugaban kasa a watan Janairu kamar yadda shugabansu, Gwamna Nyesom Wike ya yi alkawari a watan Disamba, inji rahoton Daily Trust.
Gwamnonin tsagin G5 su ne kamar haka; Wike, Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benue), Okezie Ikpeazu (Abia) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) sun sha alwashin kin yin aiki da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu, Atiku Abubakar.