Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatin sa ta dauki ma’aikatan lafiya 260 aiki; daga cikinsu, akwai Masana harhada magunguna don tabbatar da ingantaccen isar da ayyuka na kiwon lafiya, Tribune Online ta rahoto.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an kungiyar harhada magunguna ta Najeriya PSN karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Cyril Usifor da ke jihar domin kammala shirye-shiryen gudanar da babban taronsu na kasa da za a yi a Gombe.
KARANTA WANNAN: Likitocin Masu Neman Kwarewa Sun Soke Zanga-Zangar Kasa da Suka Shirya
Gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi.
Gwamnan ya kara da cewa ana shirin daukar karin ma’aikatan lafiya guda 200 domin samar da ma’aikata a asibitocin da ake shirin kammalawa a garuruwan Kaltungo, Kumo da kuma Bajoga.
Ya bayyana cewa gwamnati ta samar da akalla cibiyoyin kiwon lafiya guda daya a kowace gundumomin siyasa 114 na jihar.
Yahaya ya kara da cewa baya ga gyaran asibitin kwararru na jihar, gwamnatin da ke karkashinsa na sake farfado da manyan asibitocin Kaltungo da Bajoga yayin da ake aikin gina wani sabo a Kumo domin kawo ingantacciyar lafiya da araha ga jama’a a asibitin.
“Don samun lokaci, wadannan kadan ne daga cikin dimbin ayyukan da gwamnan jihar Gombe ya bayar kuma har yanzu yana bayar da tabbacin tabbatar da lafiyar al’umma”.
A fannin ma’ajiyar masana’antu wanda shugaban kungiyar harhada magunguna ta Najeriya PCN ya bayyana a matsayin babban darasi na gaba, wakilin gwamnan ya ce idan aka kammala shi, zai zama cibiyar masana’antu da ke da tasiri mai kyau wajen samar da ayyukan yi da kuma kima.
Inuwa Yahaya ya kuma jaddada cewa samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya mai araha ga jama’a ya kasance a kan kudurin gwamnatinsa na samun nasarar samar da tsarin kiwon lafiya na duniya.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban kungiyar harhada Magunguna ta Najeriya, Farfesa Cyril Usifor, ya ce sun je jihar ne domin shirye-shiryen babban taron su na shekara shekara (AGM) na taronsu na kasa da aka shirya gudanarwa a wani lokaci cikin wannan wata a Gombe.
Ya yabawa gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da yanayi mai kyau na kasuwanci domin masu zuba jari su yi bincike tare da yin abin arziki ga kansu da al’ummar jihar.
Shugaban na PSN ya bayyana ma’ajiyar masana’antu na Muhammadu Buhari a matsayin wani yunkuri na kawo sauyi da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta dauka na kawo ci gaban zamantakewa da tattalin arziki ga al’ummar jihar.
Ya kuma ce idan aka yi la’akari da yanayin da ake da su na saukaka harkokin kasuwanci a jihar, al’umma ba za ta bar wani zabi ba face tallata abin da jihar ke da shi ga masu zuba jari a ciki da wajen kasar nan.
A wani labarin kuma, Bayan Kai Ruwa Rana, NBA da EFCC Sun Yi Sulhu
Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA reshen Ilorin karkashin jagorancin shugabanta Barista Kamaldeen Gambari ta ziyarci ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Ilorin tare da yin alkawarin tallafa wa hukumar a yakin da take yi da cin hanci da rashawa.
DAILY POST ta tuna cewa NBA reshen Ilorin a ranar Alhamis din da ta gabata, a wata sanarwa da Aishat Omotayo Temim da Ridwan Musa, mukaddashin shugaban hukumar kuma sakataren yada labarai suka sanya wa hannu, sun zargi hukumar EFCC shiyyar Ilorin da abin da suka kira “ba bin doka da oda” tare da yin kira da a sauyawa kwamandan shiyyar, Micheal Nzekwe wurin aiki.