Gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya, ya kaddamar da kwamitin tantance hanyoyin shanu, kiwo, farauta da gandun daji a jihar domin dakile rikicin manoma da makiyaya da ke haddasa asarar rayuka da amfanin gona a jihar.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin kula da hanyoyin shanu, kiwo, farauta da gandun daji a jihar a ranar Alhamis, Gwamnan ya ce kafa wannan kwamatin ya nuna jajircewarsa wajen farfado da muhalli domin dakile illolin sauyin yanayi.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Neja Ta Bayyana Sunayen Kwamishinoni 30 da Masu Bada Shawara Na Musamman
Ya bayyana cewa, tsawon shekaru da dama, hanyoyin shanu, kiwo da kuma gandun daji sun dade suna daga cikin abubuwan da aka fi so da su, kuma suna ba da gudummawa wajen samar da nau’o’in halittu da kayayyakin amfanin gona.
Sannan ya kara da cewa cin zarafin da ake yi wa wadannan filaye yana haifar da babbar barazana ga wanzuwarsu,barazana ga daidaiton muhalli da kuma rayuwar manoma da makiyaya.
Yahaya ya ce, “A yau, yawancin hanyoyin mu na shanu an shige su ne, inda aka karkatar da hanyoyin hijirar da aka dade shekaru aru-aru, tare da sanya makiyaya cikin rikici da al’ummomin manoma.”
“Irin wannan abu yana faruwa da wuraren kiwo da gandun daji, inda akasarin su ko dai an shiga cikin su ta fuskar noma ko kuma ba a kula da su yadda ya kamata ba. Wannan halin da ake ciki ba shi da dorewa.”
”Gwamnatinmu ta fahimci mahimmancin dorewar muhalli wajen samar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummominmu.”
“Wannan ya sanar da shawararmu na haɗa batun rashin tsaro da na lalata muhalli da sauyin yanayi. Domin kuwa, tushen mafi yawan rikice-rikicen da suka danganci albarkatun ƙasa shine batun sauyin yanayi.”
“A arewacin Najeriya a yau, sare dazuzzuka da kwararowar hamada ne ke jefa al’ummomin makiyaya zuwa ciki, wanda hakan ke kawo rikici da al’ummomin manoma, da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummomi a tsawon shekaru.”
“Don magance waɗannan ƙalubalen tsaro, dole ne mu fara magance tushensu wanda shine lalacewar muhalli wanda ke haifar da sauyin yanayi da rashin bin ƙa’idodi na kowane rarrabuwa.”
A cewarsa, sun fuskanci matsalar sauyin yanayi da sakamakonsa kuma ba su da wani zabi da ya wuce daukar mataki a yanzu.
“Hakkinmu ne na hadin gwiwa mu yi taka-tsan-tsan tare da tabbatar da maido da kare kiwo, dazuzzuka da na namun daji. Don haka, kafa wannan kwamiti ya zama dole domin a sauya mummuna halin da ake ciki, da dawo da daidaiton muhallinmu, da inganta muhalli da kuma dorewar rayuwa,” in ji Yahaya.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattawa Ta Sanya Ranar Da Zata Fara Tantance Sunayen Ministoci
Majalisar dattawa ta sanya ranar Litinin ta mako mai zuwa domin fara tantance sunayen ministocin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika mata.
A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu ya aika jerin sunayen ministoci 28 da aka nada zuwa zauren majalisar domin tantancewa tare da tabbatar da su.