Hukumomi a Indiya ta Kudu sun bada umarnin a kulle Makarantu a ranar Talata, a yayinda zanga-zanga take cigaba da wakana akan sanya dokar hana sanya Hijabi a tsakanin Ɗalibai musulmi.
A makarantu a Jahar Karnaka ana fuskantar zaman ɗar-ɗar a tsakanin al’umma, a ƙarƙashin gwamnatin Indiya a jagorancin Babban Minista Narendra Modi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarki Mai daraja na daya ya rasu, bayan shafe shekaru 37 akan karagar mulki
Sabuwar zanga-zanga a ranar Talata an ga jami’ai suna harba hayaƙin tsohuwa domin korar masu zanga-zangar a wata Makarantar Gwamnati, a yayinda cincirindon Ƴan sanda a Makarantar.
Babban Minista Basavaraj Bommai yayi kira da a zauna lafiya, bayan yayi kira da a kulle Makarantun Jahar na tsawon kwanaki uku.
“Ina kira ga ɗalibai, Malamai da Shuwagabannin Makarantu da Kwalejoji dasu zauna lafiya da lumana,” inji shi.
Ɗalibai a manyan Makarantun Gwamnati an gaya masu da kada su sanya Hijabi a watan daya gabata, wannan abu daya fantsama a Makarantun Ilmi a Jahar.
A makarantu da dama suna fuskantar Allah wadai a tsakanin ɗalibai Musulmi inda suka Ɗaliban Hindu suka bayyana cewa sun lalata ilmi.