Gwamnatin Jigawa ta ce ta kashe Naira miliyan 500 wajen samar da ingantattun wuraren wanka a makarantu, asibitoci, kasuwanni, da wuraren ajiye motoci a fadin jihar.
Kwamishinan albarkatun ruwa, Alhaji Ibrahim Hannungiwa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Dutse.
Ya ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da dorewar matsayin ta a matsayin Jiha Budaddiya (ODF).
A cewar Hannungiwa, jihar na shirin zarce burin ODF na kasar nan da shekarar 2025.
Karanta nanSau Uku Ina Tsallake Rijiya Da Baya Akan Yunkurin Kisa-Natasha
Hannungiwa ya ce an samu nasarar hakan ne ta hanyar yin kokari sosai ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye-shirye masu inganci tare da hadin gwiwar ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).
Kwamishinan ya ce jihar ta kafa wani kwamiti da zai tsara hanyoyin da za a tabbatar da dorewar matsayin ta na ODF ta hanyar tabbatar da kawar da wannan barazana gaba daya.
A karkashin wannan kwamiti, za a samar da karin abubuwan jin dadin jama’a a wuraren taruwar jama’a da kuma kan manyan titunan jihar.
Gwamnatin jihar ta yi ayyuka da yawa a fannin wayar da kan jama’a kan mahimmancin amfani da bandakuna, musamman a yankunan karkara.
A wani labarin KumaMiyetti Allah Ta Sha Alwashin Fitar Da Bata Gari A Cikinsu
Jihar Jigawa ita ce jiha ta farko kuma daya tilo da ya zuwa yanzu UNICEF ta ayyana ba da bayan gida a kasar nan,” in ji shi, ya kara da cewa hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada gwamnan jihar Umar Namadi a matsayin jakadan ODF.
Ya ce ana sa ran gwamnan zai gabatar da kasida kan halin da Najeriya ke ciki a yakin da ake da ODF a wani taron da za a yi a kasar Canada.